‘Yan Shi’a: Waɗanda suka kashe ‘yansanda a Abuja sun kashe zaman lafiya – IG Egbetokun

Spread the love

Babban Sufeton ‘Yansanda na Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya ce waɗanda suka kashe dakarun rundunar biyu yayin tattakin mabiya mazahabar Shi’a a Abuja ranar Lahadi “sun kashe zaman lafiya”.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Najeriya a Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce jami’anta na tsaka da aikinsu a wani wurin bincike da ke kusa da Kasuwar Wuse ‘yan ƙungiyar ta IMN suka far musu.

Sai dai IMN ta musanta zargin, tana mai cewa mambobinta ba su kashe kowa ba yayin tattakin nasu na ranar Arba’in.

“Kisan ‘yansandan da aka yi a bakin aikinsu abin baƙin ciki ne sosai kuma wanda ba za a amince da shi ba, saboda waɗanda suka kashe su sun kawo ƙarshen zaman lafiya,” a cewar babban sufeton cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau.

“IGP [Egbetokun] ya kuma tabbabatar da zaƙuwar dakarun rundunar wajen kama sauran mutanen da ke da hannu don gurfanar da su a gaban kotu.”

Sanarwar ta ƙara da cewa sun kama mutum 97 da ake zargi da hannu a kisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *