‘Yan siyasar Najeriya na siyasantar da matsalar tsaro a ƙasar – Okonjo-Iweala

Spread the love

Babbar daraktar Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta zargi wasu ‘yan siyasar Najeriya da siyasantar da matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Yayin da take jawabi a taron shekara-shekara da ƙungiyar lauyoyin ƙasar ta shirya a birnin Legas a ranar Lahadi, tsohuwar ministar kuɗin ƙasar ta ce tsaro ne ginshiƙin samun kowane irin ci gaba a ko’ina.

“Ba za mu samu ci gaban tattalin arziki idan babu tsaro, haka kuma ba za mu samu tsaro ba dan ba mu da ci gaba”, in ji shugabar ƙungiyar WTO, kamar yadda rahotonni suka ambato ta.

Ta kuma yi zargin cewa akwai ‘yan siyasa a Najeriya da ke tunanin cewa hanyar da kawai za su bi wajen hana abokan hamayyarsu jin daɗin mulki, shi ne ƙirƙirar musu matsalar tsaro, ba tare da la’akari da asarar rayuka da dukiyoyin mutanen da ba su ji ba su gani ba.

“Abin da muka sani shi ne ‘yan siyasar ƙasarmu sun siyasantar da matsalar tsaro a ƙasarmu don cimma burinkansu na ƙashin kai, wannan kuma shi ne ya jefa ƙasarmu halin da take ciki a yanzu”.

Sanna kuma ta yi kira ga ‘yan siyasar ƙasar su daina siyasantar da matsalar tsaro ta hanyar alaƙanta ta da abokan hamayyarsu an siyasa.

Tana mai cewa dole ne ‘yan siyasar su dakatar da wannan ɗabi’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *