Yan ta’addan da suka yi garkuwa da yan kai Amarya a Katsina sun yi alkwarin sake aurar da Amarya a wani bidiyo.

Spread the love

Yan bindigar da suka sace yan kai amarya a karamar hukumar Sabuwa ta jahar Katsina , sun saki faifan bodiyon matan sama da 63, wadanda suka yi ikirarin matukar ba a biya kudin fansa ba, ba za su sake su ba.

A cikin faifan bidiyon an jiyo daya daga cikin dan ta’addan na cewa, amaryar da za a kaiwa mijinta, idan ba su biya kudin fansar ba za su aurar da ita ga daya daga cikin su.

An dai hango yan bindigar sun sanya wa, Amaryar kayan sojoji da kuma bindiga kirar AK47, rataye a wuyan ta.

Haka zalika sun nuna wata karamar yarinya da rike da bindiga, da kuma Direban motar da shima suka rataya masa bindiga.

Yawancin wadanda aka yi garkuwa da su mata ne da kuma kananan yara, kamar yadda faifan bodiyon ya nuna.

Almundahanar N21.5bn: Kotu Ta Kori Karar Da Aka Shigar Da Tsohon Hafsan Sojin Sama

Babu gaskiya kan cewa ƴan Najeriya na fuskantar barazana a Afirka ta Kudu

Matan sun yi kira ga gwamnati ta kawo mu su dauki, domin fitar da su daga halin kunchi da takura.

A makon daya gabata ne , yan bindigar suka farwa yan bikin akan hanyarsu ta kai amaryar gidan mijinta daga Dandume.

A baya shugaban karamar hukumar Dandume Alhaji Basiru Musa, ya tabbatar da kai harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *