Yanbindiga sun kashe mutum 907 cikin watan Agusta a Najeriya – Rahoto

Spread the love

Kamfanin Beacon Security da ke nazarin tsaro a yammacin Afrika ya fitar ya nuna cewa adadin mutanen da aka kashe a Najeriya cikin watan Agusta ya kai 907.

Cikin rahoton wata-wata da kamfanin ke fitarwa ya nuna cewa adadin mutanen da aka kashe a watan Agustan ya ƙaru daga 853 da aka samu a watan Yuli.

Rahoton ya kuma ce kaso mafi yawa na waɗannan kashe-kashen sun faru ne a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabashin ƙasar.

Haka kuma kamfanin na Beacon Security ya ce an samu ƙaruwar mutanen da ake sacewa domin neman kuɗin fansa a ƙasar a watan na Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin.

”An yi yi garkuwa da mutum 1,267 a watan Agusta fiye da mutum 1,035 da aka sace a watan Yulin da ya gabace shi”, a cewar rahoton.

Yankin arewa maso yammacin kasar ne kan gaba a ƙaruwar garkuwa da mutane a cikin watan, inda kaso 78 na satar mutanen aka yi shi a yankin, kuma jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina ne kan gaba a inda aka samu garkuwa da mutane, kamar yadda rahoton ya nuna.

Dangane da kashe-kashe kuwa rahoton ya ce jihar Borno ce kan gaba a inda aka samu asarar rayuka, daga nan sai jihohin Zamfara da Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *