Mutum ɗaya ya mutu a jihar Ogun da ke kudancin Najeriya yayin da ‘yanbindiga suka yi garkuwa da mutum bakwai, a cewar rundunar ‘yansanda a jihar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi a kan babban titin Sagamu-Ijebu-Ode.
Maharan da suka kai kusan bakwai, sun isa wurin ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47, in ji sanarwar da kakakin ‘yansanda Omolola Odutola ya fitar a yau Talata.
Ya ƙara da cewa sun bayyana lamarin a matsayin fashi da makami, da kisan kai, da kuma garkuwa da mutane.