Yancin ƙananan hukumomi: Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani kwamiti mai mutum 10 da zai duba shirin aiwatar da hukuncin da Kotun Ƙolin ƙasar ta yi game da bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin gashin-kai.

A ranar 11 ga watan Yulin da ya gabata ne Kotun Ƙolin ta yanken hukuncin cewa matakin da gwamnonin jahohi ke ɗauka na ci gaba da riƙe wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen gudanarwasu ya saba wa doka.

Makonni biyu da yanke wannan hukuncin Sakataren Gwamnatin Najeriya Sanata George Akume, ya kafa kwamitin domin aiwatar da wannan hukuncin.

Kwamitin da ya ƙunshi ministan kuɗi da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a da ministan kasafin kudi da tsare-tsare, da babban akanta kuɗi na ƙasa da gwamnan babban bankin Najeriya da babban sakatare a ma’aikatar kuɗi da tara haraji da wakilan gwamnonin jahohi da kuma na kananan hukumomi.

Darakta watsa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Segun Imohiosen, ya bayyana cewa babban muradin da kwamitin ya sanya a gaba shi ne tabbatar da an bai wa duka ƙananan hukomi 774 na ƙasar, ‘yancin gashin kai, ta yadda za su yi amfani da kuɗinsu ba tare da fuskantar katsalandan daga gwamnonin jahohi ba, kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya saka wa muradin ganin an bi turbar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya sharɗanta.

A tsarin rabon tattalin arziki da kuɗaɗen gudanarwar wata-wata gwamnatin tarayya na samun kashi 52.68 cikin 100, jihohi masu kashi 26.72, yayin da ƙananan hukumomi ke samun kashi 20.60 cikin 100 na kuɗin.

Masana dai na ganin za a samu sauyi ga bunƙasar ƙananan hukumomi musamman idan har suna da damar tafiyar da kuɗaɗensu, muddin babu wata hanya ta zangon-ƙasa da aka bijiro da ita, kasancewar kuma su ne suka fi kusa da talakawa.

Sai dai duk hasashen samun sauyin bayan hukuncin Kotun Ƙolin, wasu na bayyana shakku kan yadda za a tabbatar ba a yi facaka da kuɗaɗen ba kamar yadda aka yi a baya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *