Rundunar ‘yansandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta kama wani mutum da ta ke zargi da zama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Saidu Abdulƙadir.
Kwamishin ‘yan sandan birnin, CP Benneth Igwe ne ya tabbatar da kamen a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai a birnin rana Juma’a.
Kamen na zuwa ne yayin da ministan birnin tarayyar Nysom Wike ya sanya ladan nairan miliyan 20 ga duk wanda ya taimaka da bayanan da za su kai ga kama ɓata-garin da suka addabi birnin.
CP Igwe ya ce an kama mutumin ne bayan da ‘yan sanda suka kai samame sansanin masu garkuwa da ke kan iyakan Abuja da jihar Nasarawa ranar Alhamis da daddare.
Kwamishinan ya ce a lokacin da ‘yan bindigar suka ga ‘yan sandan sai suka buɗe musu wuta, inda aka yi musayar wuta, kafin daga bisani ‘yan sandan su fatattake su.
Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace ɗaliban Ekiti
An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba
”Bayan arcewar masu garkuwar ne kuma ‘yan sanda suka kuɓutar da wasu mutum biyu da suka yi garkuwa da su, tare da lalata sansanin da kuma kama jagoran masu, mai suna Saidu Abdulkadir, wanda dama ‘yan sanda sun jima suna nemansa ruwa-a-jallo”.
“Binciken farko da ofoshinmu ya gudanar ya gano cewa wanda ake zargin, shi ya kitsa harin da aka yi garkuwa tare da kisan hakimin Ketti da ke yankin ƙaramar hukumar birnin Abuja, mista Sunday Zakwai.