Yansanda sun kama mutanen da ake zargi da safarar ƙananan yara a Abuja

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta kama wani mutum da take zargi da safarar ƙananan yara kimanin 12 a cikin mota zuwa jihar Ogun.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta kama mutumin ne ranar Juma’a da rana a lokacin da yake safarar ƙananan 12 da suka haɗar da mata takwas da maza huɗu a cikin mota a kan hanyarsa ta zuwa wani wuri a jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.

Yan Bindiga Na Shirye-Shiryen Kawo Min Hari — Dikko Radda

Yan Banga Ba Su Da Hurumin Ɗaukar Doka A Hannu: Kwamishinan Yan Sanda

Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa ƙananan yaran ‘yan tsakanin shekara biyar zuwa 16, dukkansu ‘yan asalin ƙaramar hukumar Akwanga ne daga jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.

‘Yan sandan sun zargi wani fasto mai suna Simon Kado da wani mutum guda – waɗanda ta ce suna hannunsu – da hannu a safarar yaran zuwa jihar ta Ogun wa.

Rundunar ‘yan sandan Abujan ta ce tana tuntuɓar takwararta da ke jihar Nasarawa domin shirya yadda za a mayar da yaran wajen danginsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *