Yansanda sun kama mutum 254 bisa zargin garkuwa da mutane a Najeriya

Spread the love

Rundunar ‘yansanda Najeriya ta ce ta kama mutum 254 cikin mako biyu da take zargi da aikata miyagun laifuka a faɗin.

Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce rundunar ta samu gagarumin cigaba a yaƙi da aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar.

”Bisa koƙarin da rundunar ‘yansada ta yi ta samu nasara kama mutum 254 da take zargi da aikata laifuka ciki har da ‘yan fashi 92 da masu garkuwa da mutane 153 tare da mutum tara da ake zargi da aiki da ƙungiyoyin asiri”, in ji sanarwar.

Kwamitin da IGP Kayode Adeolu, Ya kafa Ya gano Mutane 300 a gidan yarin Kano, wanda babu kundin laifukan da Suka aikata.

Za mu dauki mataki a kan masu tare motocinmu suna wawar kaya – NARTO

Sanarwar ta ce ‘yansandan sun kuma kuɓutar da mutum 35 da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato ababen hawa bakwai da aka sace.

Haka kuma ‘yansandan sun kuma ce sun ƙwato bindigogi 44 tare da harsasai kusan 477 da bindigogi daban-daban.

Rundunar ‘yansanda ta ce ta ƙaddamar da samamen ne a jihohin Plateau da Cross River da Taraba da kuma birnin tarayyar ƙasar Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *