Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta ce ta kama mutum takwas da suka yi garkuwa da wasu ɗalibai da malaman makarantar Apostolic Faith a Emure-Ekiti, da ke jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar CP Adeniran Akinwale, ne ya bayyana haka lokacin da yake holen masu garkuwar a shalkwatar rundunar da ke birnin Ado-Ekiti, ranar Juma’a.
Mista Akinwale ya ce an kashe ɗaya daga cikin masu garkuwar a lokacin musayar wuta da jami’an ‘yansanda.
Kwamishinan ya ƙara da cewa maharan su ne kuma suka yi garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon. Paul Omotoso a shekara 2023
”Binciken farko ya nuna cewa Sumo Karami, tare da yaransa ne suka sace tare da yin garkuwa da ɗaliban nan da malamansu a Emre-Ekiti ranar 29 ga watan Janairu”, in ji kwamishinan.
An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba
Ya ƙara da cewa “Mun gano wayar da masu garkuwar suka yi amfani da ita wajen kira domin neman kuɗin fansa don sakin ɗaliban da malaman a hannun maharan”.
“Haka kuma an gano wasu abubuwa tare da maharan, daga ciki har da bindiga ƙirar AK-47 da wata ƙaramar bindiga da harsasai biyar a cikinta, sannan kuma da abun kurtun AK-47 21 maƙare da harsasan, sa sauran abubuwa”, in ji mista Akinwale.