‘Yansanda sun musanta zargin shirya garkuwa da mutane a Abuja

Spread the love

Yansandan Najeriya sun musanta raɗe-raɗin zargin shirya garkuwa da mutane a jami’ar Abuja.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke shirin gudanar da bukukuwan cikar ƙasar shekara 64 da samun ‘yancin kai cikin mako mai zuwa.

A ‘yan ƙwanakin nan ne dai zargin shirya garkuwa da mutane a jami’ar ya karaɗe shafukan sada zumunta.

To sai dai cikin wata sanarwa da kakakin ‘yansandan birnin Abuja, Josephine Adeh ta fitar ta ce rahotonnin shirya harin ba gaskiya ba ne.

“Rundunar ‘yansandan Abuja, na son fayyace wa al’umma cewa waɗannan rahotonni ba gaskiya ba ne, labarai ne irin na ƙanzon kurege, kuma marasa tushe, da aka ƙirƙira da nufin haifar da fargaba da tsoro a tsakanin mazauna Abuja da na jami’ar”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Josephine Adeh ta ƙasa da cewa tuni rundunar ta ƙara girke jami’an ‘yansandan da kayan aiki a faɗin birnin da kewaye.

A baya-bayan nan birnin na Abuja ya fuskanci karuwar matsalar garkuwa da mutane. Inda mazaune unguwannin da ke wajen birnin ke cewa masu garkuwar na addabarsu a wasu lokuta ba tare da ɗaukin jami’an tsaro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *