Yar Gwagwarmaya Naja’atu Muhammad Da Nuhu Ribadu Sun Fara Nunawa Juna Yatsa

Spread the love

 

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bukaci shugabar kungiyar taurarin Arewa, Hajiya Naja’atu Muhammad, da ta fito fili ta nemi afuwarsa saboda da sharrin da ta yi masa a wani bidiyo da aka wallafa a dandalin Tik Tok .

A cikin faifan bidiyon da aka sanya a Tiktok, Hajia Muhammad ta zargi mai baiwa Shugaba Bola Tinubu shawara akan harkokin tsaro, lokacin yana shugaban hukumar EFCC ya ce Tinubu yana cikin manyan barayin dukiyoyin al’umma .

A wata wasika ta hannun lauyansa, Dr. Ahmed Raji, SAN, Nuhu Ribado, ya ce a bainar jama’a ko a boye, bai taba raya irin wannan maganar a ransa ba.

Ya ce kalaman da Hajiya Naja ta yi sun jawo masa matsalar da bai san adadinta ba.

A cikin wasiƙar mai kwanan watan Fabrairu 4, 2025, kuma Dokta Raji yace dole ne Hajiya Naja ta fito ta bayyana hujjojinta, ko kuma ta fito ta janye kalaman nata tare da neman afuwarsa Nuhu Ribado.

Wasikar ta ce “Kalaman sun sanya ana kallon NSA a matsayin wani matum mai magana biyu ko fuska biyu, kuma hakan ya jawo masa matsaloli a gare shi .

 

“Mun baki kwanaki 7 daga ranar da wannan wasika ta same ki, da ki fito manyan jaridun Nigeria guda 5 domin ba da hakuri ga Nuhu Ribado ko kuma mu hadu da ke a gaban Kotu”.

Sai dai a martanin ta yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce har yanzu tana nan akan bakarta kan maganar da ta fada akan mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Nuhu Ribado.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa Nuhu Ribado ya yi barazanar maka Hajiya Naja’atu Muhammad a kotu matukar bata janye kalaman da tayi a akansa ba.

Hajiya Naja’atu Muhammad ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi da gidan Rediyon Premier dake Kano.

“Ina nan akan bakara ba zan janye kalami na ba, ballantana na ba shi hakuri, idan ya so ya kaini Kotun koli”. Inji ta

Ta ce maganar da ta fada ba karya ba ce, sai dai idan shi ne ya yiwa mutane karya lokacin da ya ke a matsayin shugaban hukumar EFCC.

Idan za’a iya tunawa dai Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce a lokacin da Nuhu Ribado yake a matsayin shugaban hukumar EFCC ya ce Tinubu cikakken dan cin hanci da rashawa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *