Yar Najeriya ta lashe azurfa a gasar nakassu ta Paralympic

Spread the love

Yar wasan Najeriya, Flora Ugwunwa ta lashe lambar azurfa a gasar jifan mashi ta mata a gasar wasannin nakassu ta Paralympic 2024 da ke gudana a birnin Paris.

Ugwunwa ta ƙare a mataki na biyu bayan da jifanta ya kai mita 19.26, bayan na Nurkhon Kurbanova, ‘yar Uzbekistan da jifanta ya kai mita 21.12.

Nasarar Ugwunwa ya sa Najeriya ta samu lambar yabo ta farko a ɓangaren jifan mashi na mata, wanda kuma shi ne lambar yabo ta huɗu da Najeriya ta samu kawo yanzu a gasar.

‘Yar wasan mai shekara 40 ta ci gaba da haskawa fagen wasanin, inda awo yanzu ta lashe lambobin yabo uku a jere a gasar nakasassu ta Paralympic, (bayan da ta lashe zinare biyu a Rio da Tokyo sai kuma yanzu ta samu azurfa a Paris)

Sauran ‘yan wasan Najeriya da suka samu lambobi a gasar kawo yanzu sun ne Onyinyechi Mark da Eniola Bolaji sai kuma Esther Nworgu.

ci gaba da haskawa fagen wasanin, inda awo yanzu ta lashe lambobin yabo uku a jere a gasar nakasassu ta Paralympic, (bayan da ta lashe zinare biyu a Rio da Tokyo sai kuma yanzu ta samu azurfa a Paris)

Sauran ‘yan wasan Najeriya da suka samu lambobi a gasar kawo yanzu sun ne Onyinyechi Mark da Eniola Bolaji sai kuma Esther Nworgu.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *