Yar Najeriya ta soma bulaguro daga London zuwa Legas a mota

Spread the love

Wata yar Najeriya Pelumi Nubi ta soma wata tafiya daga birnin Landan zuwa Legas ta mota – tafiyar da ke da nisan fiye da kilomita 7,000.

Daga Ingila, Ms Nubi za ta tsallaka Faransa da Spaniya kafin shiga Africa ta kasar Maroko.

“Bayan nan, za ta bi ta Sahara ta shiga Mauritania da Senegal da Gambia da Guinea- Bissau da Guinea da Saliyo da Laberiya da Mali da Burkina Faso da Ivory Coast da Ghana da Togo da Benin sai kuma Najeriya zuwa Legas,” in ji Ms Nubi.

Ba wannan ne karon farko ba da ake irin wannan kudiri na tafiye-tafiye da mota daga Landan zuwa Legas, sai dai Ms Nubi ta ce tana tunanin ita ce bakar fata mace ta farko da ta yi yunkurin yin haka.

Sojoji sun kuɓutar da mutum 35 tare da kashe ƴan bindiga biyu a Katsina

Yadda sojin Najeriya suka yi wa ƴanbindiga ruwan wuta ta sama

“Sai dai ta ce wannan ba batun kafa tarihi bane. Batu ne na nuna wa duniya wani abu da ba a yi tunanin za a iya ba,” kamar yadda ta ce a lokacin da ta sanar da kudurin nata a watan Nuwamban bara.

A makon da ya gabata, Ms Nubi ta ce ta dauki tsawon shekara daya tana shiri da tara kudi da kuma tsara yadda bulaguron zai kasance.

Ms Nubi wadda ke son tafiye-tafiye ta ziyarci kasa 80 kuma tana yawan nuna tafiye-tafiyen da ta yi a shafukanta na sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *