Yar Najeriyar da ke fatan zuwa Legas daga London a mota ta isa Afirka

Spread the love

Matar nan yar Najeriya, Pelumi Nubi ta isa Afirka a kokarin da take na zuwa Legas daga London a mota.

Ta tsara bi ta kasashe 17 cikin nisan Nubida bai wuce kilomita dubu bakwai ba da burin isa Legas cikin wata biyu.

Matar mai shekara 29 tana wallafa bayanan yadda bulaguron nata ke kasancewa daga Paris a Faransa bayan da ta bar Ingila a farkon watan nan.

A ranar Lahadi, ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram bayan da ta isa Moroko.

karan ta labarin Yan sanda sun kama mutum 307 a samame kan matattarar miyagu a Abuja

karan ta wannan labarin Gobara Ta Ci Ofishin ’Yan Sanda A Kano

Hanyoyin da za ta bi sun hada da Yamma da hamadar Sahara da Mauritaniya da Senegal da Gambia da Guinea Bissu da Saliyo da Laberiya da Mali da Burkina Faso da Ivory Coast da Ghana da Togo da Benin sai Najeriya inda za ta yada zango a Legas.

Ms Nubi na ganin ita ce mace bakar fata ta farko da ke wannan yunkuri.

Ta jaddada cewa burinta ba shi ne kafa tarihi ba sai dai tana son nunawa duniya cewa za ta iya abin da ba a yi zato ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *