‘Yaranmu na cikin ƙunci bayan kama su da gwamnatin Sokoto ta yi kan zanga-zanga’

Spread the love

A Najeriya, wasu ‘yan uwa da iyayenƳan sanda sun gurfanar da masu zanga-zanga kan cin amanar ƙasa a jihar Borno matasan nan da gwamnatin jihar Sokoto ke ci gaba da tsarewa a gidan gyaran hali bisa zargin su da gudanar da wata zanga-zanga bayan da ƴanbindiga suka kashe Sarkin Gobir na Gatawa Alhaji Muhammad Bawa, sun koka game da irin halin da suka ce ‘ya’yansu ke ciki tun bayan tsare su da aka yi.

 

“Wallahi yaran nan suna cikin ƙunci da kuma mawuyacin hali, kuma ana azabtar da yaran nan,” in ji wani uba.

 

Mutanen Sabon Birnin sun ce kama yaran na su ba zai rasa nasaba da siyasa ba, kasancewar akwai wadanda aka saki daga cikin wadanda aka kama bayan an tabbatar da jam’iyar kowane ɓangare.

“Akwai wasu ma ƙananan yara ne, wasu ma basu nan amman saboda basu jam’iyar gwamnati shiyasa aka kama su aka daure kuma har yanzu ba a sake su ba.”

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin Sokoto, sai dai haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.

 

Sai dai gwamnatin jihar Sokoto a baya, ta bayyana tsare su da cewa yana da alaka da karya doka ta hanyar gudanar da zanga-zanga domin domin tayar da hankali.

 

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama ma sun bayyana ci gaba da tsare mutanen a matsayin abinda ya saba ma doka.

 

Babban jami’in gudanarwa na ƙungiyar Human Right Watch a arewacin Najeriya,Ibrahim Adamu Tudun Doki, ya ce abin ya basu mamaki saboda sun yi rubuce-rubuce ga gwamnati kan kama mutanen, ” Abu duk ya zama akwai ra’ayi na siyasa, wani lokaci duk yadda za su yi su murɗa abu ta yadda gwamnati take da ra’ayi.”

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *