Yarinyar Zuma za ta auri sarki mai mata da yawa saboda ‘soyayya’

Spread the love

Ƴar gidan tsohon shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma mai shekara 21 za ta auri sarkin Eswatini, kamar yadda mai magana da yawun sarkin ya shaida wa BBC.

Matashiyar mai zuna Nomcebo Zuma ta amince ta auri Sarki Mswati III kamar yadda aka bayyana a farkon makon nan.

Sarkin mai shekara 56 yanzu haka yana da ‘aure’ da mata 11, sannan ya taɓa yin aure sau 15 jimilla.

Kakakin Eswatini, Alpheous Nxumalo ya musanta zargin ƙulla auren domin manufar siyasa.

“So makaho ne, ba ya ganin shekaru. Soyayya za ta iya ƙulluwa tsakanin mai shekara 100 da duk wanda ya isa soyayya,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Sarki – wanda ya sahfe shekara 38 a gadon sarauta – na shan suka bisa zargin mulkin kama-karya da kuma rayuwar ƙasaita da facaka da iyalansa, yayinda waɗanda yake mulka ke rayuwa cikin talauci.

Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin gidan sarautar Eswatini da gidan sarautar Zulu- Sarkin Zulu na yanzu, Misuzulu ka Zwelithini, ɗan uwan Mswati II ne.

Mista Zuma, wanda ya sauka daga mulki saboda zarge-zargen cin hanci, kuma yanzu haka yake cigaba da fuskantar tuhume-tuhume a kotu, yana ƙara samun shahara a fagen siyasar ƙasar.

Idan ana gudanar da bikin al’adar, sarkin yana da damar zaɓar wadda yake so, inda a wannan karon ya ƙyalla ido kan ƴar tsohon shugaban ƙasar.

Ya daɗe yana fuskantar suka a kan shekarun matan da yake aura, inda ko a shekarar 2005 aka zarge shi da auren wata yarinya mai shekara 17.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *