Yau ake fara gasar Champions League ta 2024

Spread the love

A yau Talata ake fara Gasar Zakarun Turai ta 2024 wanda aka sauyawa fasali.

Gasar ta bana za ta kunshi ƙungiyoyi 36

Yawan wasannin da za a fafata a sabon tsarin zai ƙaru daga 125 zuwa 189.

Kuma kowace ƙungiya za ta buga wasanni takwas – maimakon shida da aka saba yi – a zagayen farko na gasar.

Masu sharhi kan wasannin kwallon kafa dai na ganin cewa ƙungiyoyin da ke gaba-gaba wajen lashe gasar ta bana su ne mai rike da kofin bara Real Madrid ganin cewa sun ƙara wa tawagarsu karfi ta hanyar kawo zakarurin ɗan wasa Kylian Mbappe, sai kuma Man City wanda Pep Guardiola ke jagoranta.

Ana kuma ganin ƙungiyoyi irin Bayern Munich da Liverpool da Bayern Leverkusen da Inter Milan da kuma Atletico Madrid su ma suna da damar lashe gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *