Yau ake rantsar da Putin a matsayin shugaban Rasha karo na biyar

Spread the love

A yau ake bikin rantsar da Vladimir Putin a matsayin shugaban Rasha karo na biyar.

Nasararsa a zaɓen watan Maris na zuwa ne makonni da mutuwar fitaccen abokin hamayyarsa, Alexei Navalny, a gidan yari.

Wakilin BBC ya ce kusan shekara 25 yanzu da Putin ke mulki a Rasha a matsayin shugaban ƙasa ko shugaban gwamnati

Ƙasashen yamma sun yi alla-wadai da zaɓensa a wannan lokaci da suka ce babu sahihanci da daraja dimokuraɗiyya.

Ƙasashen Amurka da na Tarayyar Turai sun ce za su ƙauracewa bikin da aka shirya a Kremlin – kodayake Faransa da wasu ƙasashen na Turai za su tura wakilai duk da roƙon da Ukraine ta yi cewa su yi biris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *