Yau ake sa ran sakin ministocin Bazoum huɗu da sojoji suka tsare a Nijar

Spread the love

A yau ake sa ran sako wasu tsofaffin ministoci guda hudu na tsohuwar gwamnatin hamɓararen shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar, Bazoum Mohamed.

Wata babbar kotun sojoji ce da ke Yamai, babban birnin ƙasar ta amince da sakin tsoffin ministocin a jiya Litinin.

Sai dai kuma sakin nasu zai samu idan har babban lauyan gwamnati bai yi kira da a sake duba matakin ba.

Tsofaffin ministocin guda huɗu sun haɗa da Elhadji Ibrahim Yacoubou, ministan ƙasa kuma ministan makamashi da wutar lantarki kuma shugaban jam’iyyar NPN ƙishin ƙasa da Dakta Rabi’ou Abdou, tsohon ministan tsare-tsare da Dakta Ahamet Djidoud, tsohon ministan fasali ta ƙasa da Dakta Hama Souley, tsohon ministan harkokin cikin gida.

Fatan al’ummar Nijar a yanzu shi ne, gwamnatin soji ta Nijar ta sako duka mutanen da aka kama ba tare da jingina masu laifi ba sannan waɗanda aka kama kuma, a gurfanar da su gaban kuliya don su fuskanci shari’a tare da tilasta masu biyan kuɗin gwamnati da suka yi rub da ciki da su.

Masu nazarin al’amuran yau da kullum sun buƙaci a gudanar da taron yafe wa juna na ƴan ƙasa don a kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya don ci gaba da gwagwarmaya ta harkar sojoji da farar hula.

An dai kama tsofaffin ministocin da wasu muƙarraban hamɓararriyar gwamnatin kwana ɗaya bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Bazoum saboda zarginsu da kalaman cin amanar ƙasa da kuma yin zagon ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *