Kuɗaɗen shiga da Najeriya ke samu daga bangaren masana’antu na fitar da kayayyaki ya ragu da kashi 166 cikin 100 zuwa naira 778.4bn daga adadin da ya kai naira tiriliyan 2.2 a shekarar 2019.
Tun daga shekarar 2019, yanayin ya koma ƙasa, tare da raguwa sosai zuwa naira 960.7 biliyan a cikin 2020 saboda cutar COVID-19 yayin da aka samu murmurewa a shekarar 2021 a kan naira triliyan 1.15 inda a shekarar 2022 kuma aka sami raguwa mai yawa zuwa naira biliyan 781.1 kuma raguwar naira biliyan 778.4 a 2023.
Babban bankin ya dora alhakin raguwar kasuwancin ketare a kasar kan rashin kyawun ababen more rayuwa da kuma rashin ingantaccen kayan aiki da dai sauransu.
Rahoton ya ce kuɗin da ake samu daga kasuwanci a Najeriya da Habasha ya ninka wanda ake samu a Amurka sau hudu zuwa biyar saboda rashin tsaro da tsadar sufuri da yanayin kasa da kuma rashin ingancin hanyoyi.
“Nazari daga yankin Afirka a koyaushe yana samun bambance-bambance a cikin farashin kayayyakin da ake shigowa da su na kayan abinci da wanda baabinci ba da kuma kayan amfanin gona da kuma farashin dillalan kayayyaki.
- Yan Sanda Sun Cafke Magidanci Bisa Zargin Shirya Taron Gangi Da Ya Janyo Rikicin Fadan Daba A Kano.
- An Fara Bincike Kan Dalilin Da Ya Sanya Jami’in Kwastam Ya Harbe Kansa A Kano
“Misali, farashin ciniki ya ninka sau hudu zuwa biyar a Habasha da Najeriya fiye da na Amurka, saboda rashin kyawun ababen more rayuwa da karancin gasa a fannin sufuri, da kuma yanayin kasa,” in ji rahoton.
Rahoton ya kuma kara da cewa, illar wadannan ƙalubalen, sun hada da fifita masana’antun Afirka su sayar da kayyayaki a cikin gida maimakon fitar da su zuwa kasashen waje.
Masu masana’antu da masu gudanar da ayyukan fitar da kayayyaki sun koka kan yadda yanayin kasuwanci a kasar ya yi kamari yana sa kayayyakin cikin gida ba su da gasa a duniya.
Rahoton na bankin ya zo ne bayan da hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta Najeriya (NEPC), ta bukaci masu fitar da kayayyaki daga Najeriya su bi ka’idojin fitar da kayayyaki zuwa kasashe daban-daban.
a zuwa naira biliyan 781.1 kuma raguwar naira biliyan 778.4 a 2023.