Adadin marasa aikin yi a Najeriya ya karu zuwa kashi biyar cikin 100 a rubu’i na uku na shekarar 2023, daidai lokacin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa bayan da gwamnati ta cire tallafin man fetur.
Shugaba Bola Tinubu ya kare manyan sauye-sauyen da ya yi guda biyu da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa da tantance darajar naira, inda ya ce duk da cewa hakan zai haifar da wahalhalu na kankanin lokaci, suna da muhimmanci wajen samar da masu zuba hannun jari da habaka kuɗaɗen gwamnati.
Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta ce adadin marasa aiki ya tashi daga kashi 4.2 cikin 100 a cikin kwata na baya.
Ecowas na tunanin yadda za a sassanta da Nijar da Mali da Burkina Faso
Kotu ta yi umarnin likitoci su duba kwakwalwar Yar Tiktok Murja Kunya
Adadin marasa aikin yi a tsakanin matasa masu shekaru 15-24 ya tashi zuwa kaso 8.6 daga kaso 7.2.
Rashin aikin yi a cikin birane shi ma ya ƙaru kaɗan zuwa kaso 6 daga kaso 5.9 a rubu’in da ya gabata.
Najeriya wadda ita ce ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka mai sama da mutane miliyan 200, ta yi fama da marasa aikin yi tsawon shekaru da dama, sakamakon ƙaruwar yawan al’umma da ya zarce ci gaban tattalin arzikin ƙsar.
Adadin ayyukan yi na yau da kullun, wanda ke auna yawan ma’aikata a cikin tattalin arziki ya sami canji kaɗan da kaso 92.3, a cewar NBS, aikin ma’aikata shi ma ya faɗi kaɗan zuwa kaso 79.5 daga kaso 80.4 a cikin kwata na biyu.