An rufe rumfunan zaɓe bayan kammala kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar ranar Asabar.
Tuni aka fara ƙirga ƙuri’a a matakin rumfunan zaɓen.
Rahotonni na cewa an gudanar da zaɓen ba tare da matsala a wurare da dama a faɗin jihar.
A yanzu hankula sun fara karkata kan cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen, domin tattara sakamakon a matakin ƙaramar hukuma kafin daga bisani a tattara a matakin jiha.
BBCH