Za A Binciki Kwakwalwar Mutumin Da Hau Kan Eriyar Gidan Radio A Abuja

Spread the love

Rundunar ‘Yansandan Najeriya ta ce ta tura mutumin nan da ya hau kan eriyar gidan rediyo zuwa cibiyar gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa.

A ranar Litinin ne mutumin mai suna Shuaibu Yushau ya hau kan dogon ƙarfen da ke kan dutsen Aso da ke Abuja babban birnin ƙasar, yana mai cewa ba zai sauko ba har sai gwamnati ta sauƙaƙa wa ‘yanƙasa rayuwarsu.

Sai da jami’an tsaro suka shafe lokaci suna lallaɓa shi kafin ya sauko daga kan eriyar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansanda reshen Abuja ta fitar ta ce za su kai shi kotu da zarar an tabbatar lafiyarsa ƙalau.

“Idan gwaji ya tabbatar lafiyarsa ƙalau, za mu tuhume shi a kotu da laifin yunƙurin kashe kansa, da kuma tayar da ruɗani da haɗa husuma,” a cewar Josephine Adeh.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *