Za a daina dogayen layuka idan ƴan kasuwa suka fara sayen man mu – Dangote

Spread the love

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce za a daina samun dogayen layuka a gidajen mai muddin dillalan mai suka fara sayen mai a matatarsa.

Dangote ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da shugaba Bola Tinubu a yau Talata.

Hamshaƙin attajirin na Afrika ya kuma buƙaci babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, da kuma ƴan kasuwa a faɗin ƙasar da su daina shigo da mai daga waje.

Ya ce matatarsa ita ce mafita ga batun dogayen layuka da ake samu a gidajen mai da ke faɗin ƙasar.

“Kiyasin da na yi ya nuna cewa fetur da za mu iya sha a kullu yaumin zai kai lita miliyan 30-32, za mu iya fara bayar da wannan ko a mako mai zuwa. Ba wani abun damuwa bane saboda muna da lita miliyan 500 a tankokinmu yanzu haka. Don haka ko ba a shigo da mai cikin ƙasa ba, za a iya amfani da man mu a faɗin ƙasar har na tsawon kwanaki 12,” in ji Dangote.

Hakan na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan da gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da tsarin sayar da ɗanyen man fetur a naira ga Dangote maimakon kuɗin dala.

Gwamnatin tarayya ta ce matakin zai daidaita farashin man fetur a ƙasar da kuma karfafa kuɗin naira ta hanyar rage buƙatar amfani da dala wajen hada-hadar ɗanyen man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *