Za A Dinga Fassara Wa Kurame Sanarwar Rundunar Yan Sandan Kano.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, za ta Fara aiki da wani jami’inta , da ya kware wajen fassara yaren Kurame, don sanar da masubukata ta musamman halin da ake ciki.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka ta cikin wani faifen bidiyo da wallafa a shafinsa na Facebook, a Ranar Juma’a.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce, jami’in dan sandan mai suna PC Ibrahim Danbaba, zai yi aiki tare da shi, a duk lokacin da za su yi Wata sanarwa, ko yin Kira ga mutane, musamman kan abunda ya shafi harkar tsaro, inda zai dinga fassara wa zuwa yaren Kurame.

Kwamishinan Yan Sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya godewa al’ummar jahar, bisa hadin Kai, da kuma addu’o’in da suke yi a koda yaushe, kamar yadda jaridar, DONGARI.NG, ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *