Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan kare lafiya ba, to akwai yiyuwar mazauna Abuja, Kano, da sauran jihohin Arewa da dama za su fuskanci tsananin zafi wanda zai shafi lafiyarsu.
Tsananin zafi dai na janyo cutuka da dama waɗanda za su iya kai wa mutuwa, kuma hakan a faruwa ne a lokacin da jiki ya kasa sarrafa zafin.
Mazauna waɗannan jihohin na iya fuskantar matsanancin zafi, wanda zai sa su shiga yanayi mara kyau, a cewar Nimet.
- Maniyyata 51,447 ne za su sauke farali a aikin Hajjin bana – NAHCON
- Sojojin sun yi wa ‘yan bindiga kwantan ɓauna, sun kashe uku a Kaduna
“Mun sake shiga lokacin zafi. Ya kamata jama’a su ɗauki matakan da suka dace,” kamar yadda “NiMET ta yi gargaɗi.
Ta ce Abuja, Kano, Sokoto, da Kogi ne za su fi fuskantar tsananin zafi, inda ta shawarci mazauna yankunan da su ɗauki matakin kariya da ya kamata.
Wasu jihohin da ke cikin rukunin fuskantar zafin sun haɗa da Kebbi, Katsina, Adamawa, Gombe, Bauchi, Taraba, Neja, Zamfara, Nasarawa, Jigawa, Benue, da kuma Kwara.
NiMET ta kuma gargaɗi mazauna jihohin Osun, Ekiti, Ondo, Bayelsa, Akwa Ibom, Anambra, Delta, Enugu, Edo, Ogun, Plateau, Borno, Imo, Abia, da Cross River da cewa su kasance cikin shiri don karuwar zafi, duk da cewa zafin ba zai yi tsanani ba kamar na sauran jihohi.
Shawarwarin Nimet na yadda za a gujewa tsananin zafi
- A rika shan ruwa a-kai-a-kai
- A rika zama a wuraren da ke da sanyi domin hutawa
- Kada a bar yara a cikin mota a rufe idan ba ta tafiya
- Ka saka bakin gilashi da malafa idan za ka fita waje
- Ka saka kaya marasa nauyi kuma masu shara-shara
- Kada ka shiga rana, sannan kada a fita waje tsakanin karfe 12 na rana zuwa 4 na yamma.
- Kotu ta nemi ƴansandan New York su biya matan da suka tilasta wa tuɓe hijabi diyyar $17.5
- Dangote Ya Koma Matsayi Na 129 A Jerin Attajiran Duniya — Forbes