Za a gina babbar cibiyar lantarki mai amfani da rana a Najeriya

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta sa hannu kan wata yarjejeniyar gina cibiyar samar da wutar lantarki mai amfani da ruwa da hasken rana da za ta samar da wuta mai ƙarfin megawatt 20.

Shirin samar da lantarki mai ƙarfin megawatt 300 wani ɓangare ne na ƙudurin Najeriya na komawa ga amfani da makamashi mara gurɓata muhalli.

Za a gina cibiyar a Shiroro da ke jihar Neja a tsakiyar Najeriya kuma zai zama shirin haɗin gwiwa tsakanin kamfanin NSP mai zaman kansa da hukumar NSIA mai bibiyar harkokin gwamnatin a Najeriya.

“Wannan wani shiri ne na farko na samar da lantarki mai amfani da hasken rana da ruwa,” in ji mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Ya ƙara da cewa shirin zai taimaka wa Najeriya ta faɗaɗa hanyoyin da take amfani da makamashi.

Najeriya dai na fama da matsalar rashin tsayayyiyar wutar lantarki tsawon shekaru duk da kasancewarta babbar mai samar da iskar gas da man fetur.

An ƙarkare binciken zargin zubar da ciki da sojojin Najeriya ke yi a asirce

Yan bindiga sun aikata kazamin kisa kan masu shirin buɗa baki a Zamfara

Lamarin yana yawan janyo matsala a babban layin da ke samar wa ƙasar wuta tare da jefa jama’a cikin duhu.

Galibin mutane a yanzu suna komawa amfani da injin janareto da wutar sola mai amfani da hasken rana domin kaucewa yawan dogaro ga babban layin wutar da ke yawan fuskantar matsala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *