Kotun Shari’ar addinin musulinci mai namba 2 dake zaman ta, a Kofar kudu gidan Sarki Kano, ta bayar da umarnin tsare Wani matashi mi suna Nasiru Muktar, Wanda yake sana’ar wanki da guga, bisa Zargin sa da shiga masallacin juma’ar Unguwar Tudunwada, ya cakume Limamin masallacin tare kai masa farmaki da kuma gwajin karfi.
Laifin da Ake tuhumar matashin ya saba da sashi na 165 da 166 na kundin SPCL.
Mai gabatar da kara na Kotun, Aliyu Abidin (LLB) ya karanto masa kunshin tuhumar da ake Yi masa, Inda nan ta ke ya musanta Zargin.
Tun a ranar 22 ga watan Oktoba 2024 da misalin karfe 5:00am na Asuba Wanda Ake Zargin ya shiga masallacin juma’ar Unguwar Tudunwada, Inda ya ci kwalar limamin Mai suna Malam Murtala Sulaiman, a lokacin da yake gabatar da sallar Asubashi, tare da fisge amsa kuwa da kuma yaga masa Riga sannan ya Tsinka masa Mari lokacin da yake Ruku’i.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa, bayan faruwar lamarin ne limamin masallacin, yaje ya shigar da korafi a sashin binciken manyan laifuka dake shelkwatar Rundunar Yan Sandan Kano su kuma suka Gurfanar da shi.
Lauyan Wanda Ake Zargin ya roki Kotun da ta Sanya shi a Hannun beli, Inda kotun ta jingine rokon tare da bayar da umarni a aike da Takadda zuwa asibitin kula da masu larular kwakwalwa dake Dawanau don tabbatar da lafiyarsa ko akasin haka.
Alkalin kotun Mai shari’a Malam Isah Rabi’u Gaya, ya dage ci gaba da sauraren Shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Nuwamban 2024 , tare da bayar da umarnin tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.