Za a iya yaƙar rashawa da cin hanci a Najeriya — EFCC

Spread the love

Hukumar da ke yaƙi da rashawa da cin hanci a Najeriya, EFCC ta ce za a iya samun galaba a kan rashawa da cin hanci a ƙasar duk kuwa da irin ƙaruwar da yake yi.

Sai dai shugaban hukumar Ola Olukayode ya ce hakan zai iya yiwuwa ne kawai idan har dukkanin masu ruwa da tsaki a fagen yaƙi da rashawa da cin hanci sun haɗa ƙarfi da ƙarfe.

Mista Olukayode wanda ya bayyana hakan a wani saƙonsa na babbar sallah, ya ce sabunta ƙudurin yaƙar dukkannin nau’in yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa abu ne mai matuƙar muhimmanci.

Shugaban ne EFCC ya ƙara da cewa “ƴan Najeriya ba su gaji rashawa da cin hanci kuma ba mu da wata matsala a matsayinmu na ƙasa.”

Daga ƙarshe Mista Olukayode ya buƙaci yan Najeriya da su yi amfani da darussan sallar Idi babba wajen gyara alaƙa da ubangiji ta hanyar kawar da rashawa da cin hanci.

“Ya kamata mu rungumi darussan haƙuri da sadaukarwa da imani da kuma kyautata tsammanin ga Allah da Idi ke koyarwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *