Ministan sufuri na Najeriya Sanata Sa’idu Alƙali ya ce za a kammalakashi na farko na aikin layin dogo da ya tashi daga Kano zuwa Maraɗi mai nisan kilomita 387 a shekarar 2025.
Sanata Alƙali ya bayyana hakan ne a lokacin da yake duba aikin layin shimfiɗa layin dogo na zamani da ake yi tsakanin Kano zuwa Maraɗi da na Kano zuwa Kaduna.
Ministan ya ce wannan shi ne karo na biyu da yake zuwa duba aikin a Kano, tun bayan da aka naɗa shi ministan.
Gwamnatin da ta gabata ce dai ta bayar da aikin gina titin layin dogo daga Abuja zuwa Kano da na Kano zuwa Maraɗi.
- Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga da lalata mafakarsu a Kaduna
- Kungiyar Malaman Kwalejin Shari’a Ta Mallam Aminu Kano Ta Rufe Makarantar Bayan Dakatar Da Dalibai Rubuta Jarrabawa.