Za a rufe ma’aikatun da suka gaza samar da kaso 5 cikin 100 na guraben aiki ga masu bukata ta musamman daga Janirun 2024

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirin ta na rufe dukkanin ma’aikatu ma su zaman kansu, da suka gaza samar wa masu bukata ta musamman kaso 5 cikin 100 na guraben aiyuka a ma’aikatun su daga ranar 17 ga watan Janairu 2024.

Babban Sakataren hukumar ma su bukata ta musamman (PWDs) na kasa James David Lalu ne, ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja lokacin da yake gana wa da manema labarai.

James Lalu ya ce dokar ta ma su bukata ta musamman ta umarci kafanoni su samar da kaso biyar cikin dari na ma’aikatansu da aka kebe domin masu bukata ta musamman.

Masu bukata ta musamman sun sha koka wa kan yadda wasu kafanoni da wasu ma’aikatun gwamnati suka ware su duk da basirar da Allah ya yi mu su da kuma ilimin da suke da shi.

Sun kara da cewa matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a halin yanzu na kara haifar da matsaloli, inda suka bukaci gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su kawo mu su dauki.

Sun bayyana hakan ne a wajen wani taron tuna wa da ma su bukata ta musamman ta duniya ta shekarar 2023 a Jos babban birnin jahar Plato.

Taron wanda wata kungiya mai suna Get Them Young Initiative ta shirya domin neman tallafi kan muhimman batutu wa da suka shafi ma su bukata ta musamman.

Shugaban kungiyar neman mafita ga masu bukata ta musamman reshen jahar Kano, Abdulrrazak Ado Zango, ya shaida wa idongari.ng farin cikin su ga me da matakin na gwamnatin tarayya ga ma’aikatu ma su zaman kansu da ma na gwamnati.

Abdurrazak Zango ya kara da cewa, akwai bukatar makarantu , kasuwanni , ofisosin yan sanda , Asibiti da kuma Kotuna , wajen samarwa da wadanda za su iya karbar ma su bukata ta musamman dan warware mu su matsalolin su cikin sauki ba tare da sun wahala ba.

Sai dai ya bayyana takaicin sa, kan wasu guraren aiki da ba a samun wadanda za su iya fahimtar abunda ma su bukata ta musamman suke bukata, inda ya ce a wasu lokutan sukan fuskanci matsala Asibiti ko kotu kasancewar babu wanda zai iya yin Magana da su.

Tun a lokacin tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari aka amince da dokar ta bayya wa ma su bukata ta musamman kaso biyar cikin dari a ma’aikatu na gwamnati da ma su zaman kansu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *