Za a sanya harajin mallakar kyanwa a Kenya

Spread the love

Mutanen da suka mallaki kyanwa ko mage ko kuma mussa a Nairobi, babban birnin Kenya, na ta nuna damuwa kan abin da suke gani wani shiri na gwamnati na sanya harajin mallakar dabbar.

A dokokin da hukumar birnin ke shirin yi, za a bukaci duk wani mai kyanwa ya yi wa dabbar tasa rijista.

Hakan zai bukaci mutum ya biya kudin lasisin mallakarta Sulai 200 (na kasar) kwatankwacin dala 1.50 ko fam 1.20 a duk shekara tare da shedar cewa an yi wa dabbar rigakafin cutar hauka.

Bayan haka, dole ne kowane mai kyanwa ya dauki alhakin halayyarta ko abin da ta yi – kamar yawo a gari ko unguwa, sannan mutum ya tabbatar ba sa kara ko kuka da zai damu jama’a.

Bugu da kari, dole ne idan kyanwa tana cikin lokacin bukatar barbara, mai ita ya tsare ta a waje daya.

Hukumomi sun ce za a yi dokar ne domin inganta hanyoyin kula da lafiyar maguna, abin da wasu ke suka a kai.

A kwanan nan Kenya wadda ke gabashin Afirka ta yi fama da tarzoma a kan kara haraji da gwamnati ta yi, har ta kai matsi ya sa ta janye karin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *