Za A Yankawa Mutanen Da Ba Su Da Abinci Giwaye 200 A Zimbabwe

Spread the love

Hukumomi a Zimbabwe sun ce za su zaɓi giwaye 200 da za a yanka domin raba naman su ga mutanen ƙasar da ke shan wahala wajen samun abinci saboda tsananin fari.

Kudancin Afirka na fama da tsananin fari, wanda ƙwararu suka ce shi ne mafi muni a tarihi shekaru masu yawa.

Zimbabwe za ta zamo ƙasa ta biyu a yankin da ta yanka giwaye domin raba wa jama’a naman su a bana, bayan Namibia, wadda ta yanka giwaye fiye da 80 a watan da ya gabata.

Zimbabwe tana da giwaye aƙalla dubu ɗari, kuma ita ce ƙasa ta biyu da ta fi yawan giwaye a duniya, bayan Botswana.

Shekara 35 baya dai ƙasar ta taɓa yanka giwaye domin raba naman su ga mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *