Za a yanke hukunci kan hurumin kotu a rikicin masarautar Kano ranar 13 ga watan nan

Spread the love

Babbar kotun tarayya da ke Kano ta sanya ranar 13 ga watan nan na Yuni domin bayyana hukuncinta a kan ko tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar gabanta kan rushe masarautu biyar a jihar ko kuma ba ta da hurumi.

Tun da farko kotun ta bukaci bangarorin biyu su yi mata bayani kan ko tana da hurumin ko kuma a’a inda kowanne bangare ya yi bayani tare da kafa hujjoji da irin shari’o’in da suka gabata kan rikicin masarautu a ƙasar.

Lauyan ɓangaren gwamnatin Kano ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da karar ma ba shi da hurumin neman kare masa hakki saboda dokar da ta ba shi damar zama ɗan majalisar sarki an rushe ta.

To amma lauyan mai ƙara ya ƙalubalanci hakan da cewa, idan ana batu na take haƙƙin ɗan’Adam to al’amari ne da ba shi da iyaka don haka kotun ta ci gaba da sauraron wannan Shari’a.

Bayan sauraren doguwar mahawarar daga dukkanin ɓangarori biyun alƙalin kotun AM Liman, ya sanar da ranar da kotun za ta yanke hukunci kan wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *