Allah ya yi wa Hajiya Hajara (Uwani) rasuwa, mahaifiyar tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, kuma mamallakin gidajen Radio da talabijin na MUHASA , Muhammad Babandede.
Hajiya Hajara ta rasu a babban Asibitin Malam Aminu Kano da yammacin ranar Alhamis, 26 ga Disamba 2024.
Za’a yi Jana’izarta ranar Juma’a 27 ga Disamba 2024 da karfe 10 na safe a Masjid Zhera Zoo road Kano
Ta rasu bayan ta shafe shekaru da dama a duniya, ta bar ‘ya’ya da jikoki.
Muna fatan Allah ya gafarta mata ya sa Aljanna makoma.