Shugaban hukumar zaɓe na jihar Kano, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya ce sai an yi wa kowanne ɗan takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi gwajin ƙwaya kafin a bashi damar tsayawa takara.
Farfesa Malumfashi, ya sanar da hakan ne a yayin wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a Kano a ranar Alhamis.
A yayin taron, hukumar zaben ta sanar da cewa duk mai son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma a zaɓen to zai sayi fom a kan naira miliyan 10.
Yayin da ɗan takarar kansila kuma kuɗin fom ɗinsa ya kama naira miliyan biyar.
Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar ne a ranar 30 ga watan Nuwambar 2024.