Za mu ɗauki matakin shari’a kan ƴan siyasa da suka tayar da tarzoma’

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana zargin wasu ‘yan siyasa da hannu da tarzomar da ta ɓarke yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar.

Hukumomin sun ce za su yi duk mai yiwuwa a karkashin damar da doka ta basu don tabbatar da cewa waɗanda suke da hannu wajen kunna wutar rikici a lokacin zanga-zangar sun fuskanci shari’a.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarz shi ne mataimakin gwamnan Kano kuma ya shaida wa BBC cewa tuni suka tattara bayanai akan wadanda suke zargi kuma za su ɗauki mataki na gaba.

“Ba zargi muke ba muna da takamaiman shaida da hujja na ƴan siyasa da suka shiga suka kawo ƴan iska suka kawo ƴan ta’adda, suka biya su kuɗi suka zo suka yi wannan ta’annati, muna kuma tattara bayanai.”

Tura ta kai bango —Masu zanga-zanga

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana zargin wasu ‘yan siyasa da hannu da tarzomar da ta ɓarke yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar.

Hukumomin sun ce za su yi duk mai yiwuwa a karkashin damar da doka ta basu don tabbatar da cewa waɗanda suke da hannu wajen kunna wutar rikici a lokacin zanga-zangar sun fuskanci shari’a.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo shi ne mataimakin gwamnan Kano kuma ya shaida wa BBC cewa tuni suka tattara bayanai akan wadanda suke zargi kuma za su ɗauki mataki na gaba.

“Ba zargi muke ba muna da takamaiman shaida da hujja na ƴan siyasa da suka shiga suka kawo ƴan iska suka kawo ƴan ta’adda, suka biya su kuɗi suka zo suka yi wannan ta’annati, muna kuma tattara bayanai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *