Za mu bai wa masu zanga-zanga a Najeriya kariya – Ƴansanda

Spread the love

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce za ta bai wa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar kariya, sai dai ta ce za ta ɗauki duk wasu matakan hana ɓarkewar rikici.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, kwanaɗaya kafin zanga-zangar tsadar rayuwa da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC) ta kira a faɗin ƙasar.

A cikin sanarwar wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar ƴansandar ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce “Rundunar ƴansanda na sane da ƴancin da al’umma ke da shi na yin zanga-zanga cikin lumana kamar yadda doka ta tanada.”

Gumurzu tsakanin ƴanbindiga ya kai ga kisan gaggan ƴanfashin dagi a Zamfara

Ma su hakan Kabari sun roki gwamnatin Kano ta fara biyan su Alawus

Sai dai rundunar ta ce “yayin da take martaba ƴancin yin zanga-zanga cikin lumana, rundunar ƴansandan ta Najeriya ta ce za ta sanya ido kan duk wanda ya shiga zanga-zangar da mummunar manufa.”

“Sabida haka, rundunar ta ce ba za ta ɓata lokaci ba wajen murƙushe su ta duk hanyar da ba ta saɓa wa doka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *