Za Mu Binciko Wadanda Suka Yada Hotunan Karya Don A Zagi Yan Sandan Kano: CP Salman Dogo

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Kano ta musanta wani rahoton hotuna da ake yada wa a shafukan sada zumunta, dangane da wadanda ake zargi da aikata sata da kayayyakin da suka sata, a shagunan jama’a, gidaje da kuma ofisoshi da sunan, sun fito zanga-zangar da aka shirya yi daga ranar daya ga watan Augustan 2024.

Rundunar yan sandan jahar ta ce bayan sun kama mutanen da kuma abubuwan da suka sata ne wasu marasa son zaman lafiya, da yunkawo matsala a jahar don su hada yan sanda da al’ummar gari fada, inda suka dauko hotunan suna cewar an kama matasan ne tun a shekarar 2011 kakakin rundunar yan sandan SP Abdullahi Kiyawa ya yada su.

Sai dai mai magana da yawun  rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana wa idongari.ng, cewa a shekarar 2011 ma bai shiga aikin yan sanda ba, domin shi ya fara aiki ne a ranar 9 ga watan Disambar 2012.

‘’ abubun mamaki wadannan matasan da aka kama hotunan da rigunan duk ga sunan yanzu kwana daya kacal da kama su’’ SP Abdullahi Kiyawa’’

Kiyawa ya kara da cewa abunda mutanen suke yada karya ce kawai da bata da tushe balle makama, ma su yi din sunyi hakanne don hada bada da yan sanda da kuma al’ummar gari.

‘’ za mu ce sunji kunya domin mu na samun hadin al’ummar Kano , kuma insha Allah za mu ci gaba da yin aikin mu bisa gaskiya da rikon amana daidai gwargwadon yadda za mu iya’’ cewar SP Abdullahi H Kiyawa’’.

Kwamishian yan sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba, ya bada umarnin a binciko tare kama wadanda ake zargi da yada labaran karya a shafukan sada zumunta don a zagi yan sanda da rage mu su kwarin gwiwar aiki sannan a dinga jin haushin su.

Ya ce mutanen ba ma su son zaman lafiya ba ne, inda ya gargadi jama’a da su guji yada labaran karya da kuma abubuwan da za su haifar da tashin hankali da tarzoma musamman a wannan lokaci da wasu ke yada abu ba tare da sun bincika ba a shafukan sada zumunta.

A jiya dai bayan fara gudanar da zanga zangar, ta rikide zuwa tashin hali da kuma satar kayan mutane, inda rundunar ta kama mutane 326, mada da mata harma da kananan yara.

Kiyawa ya ce kayan da aka kwato a hannun mutanen sna da yawa ciki harda bindigu kirar AK47, jarkokin mai, kayan abinci da dai sauransu.

A karshe rundunar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike da kuma tattara shaidu za su gurfanar da su a gaban kotu don ya zama izina ga ma su son fito wa da irin wannan siga don su illata  mutane ta hanyar sace mu su kaya.

Rahotannin da Idongari.ng, ta samu na cewa wasu daga cikin mutanen da aka barnata wa dukiya suna kwance a gadon asibiti.

Saurari murya SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin yan sandan Kano

HOTUNA

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *