Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan diyyar masu taron Mauludin da harin bom daga jirgin soja ya kashe a Jihar Kaduna.
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ne ya sanar da haka, sa’o’i kadan bayan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin.
Ministan ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro da Gwamnatin Kaduna za su yi aiki tare wajen gudanar da bincike kan abin da ya faru a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Harin dai ya auku ne a lokacin da wata makatar Islamiyya take gudanar da bikin Mauludi a daren Lahadi a kauyen Tudun Biri, inda ta karbi bakuncin mahalartar daga kauyukan da ke kusa da su.
Ana tsaka da taron ne wani jirgi mara matuki mallakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya yi mahalarta taron ruwan bama-bamai.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 85 a harin baya ga wasu 66 da suka samu raunuka.