Za mu ci gaba da sayar da sumunti 3,500 – BUA

Spread the love

Shugaban kamfanin BUA, AbdusSamad Rabi’u, ya ce kamfanin zai cika alkawarinsa na ci gaba da sayar da sumunti kan farashin 3,500 daga watan Janairun 2024.

Ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan ziyara da ya kai wa shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Legas ranar Alhamis.

Ya ce kamfanin zai kuma tabbatar da cewa sumuntin ya wadata da kuma sauki ga kwastomominsa duk da kalubale da ake ciki.

“Mun saka farashi sumuntin kan naira 3,500 a kan kowane buhu. Za mu duba kuɗin haraji da kuma nisan yankin da za a kai sumunti.

“Kamar yadda ka sani, muna da kamfanoni guda biyu; ɗaya a Edo, yayin da ɗaya muke yake jihar Sokoto. Alal misali, idan kana son mu kai maka sumunti daga Sokoto zuwa Legas ko Adamawa ko kuma Maiduguri, idan ka duba yana da nisan gaske,” in ji BUA.

Ya ce duk da cewa idan aka yi la’akari da nisa ko kuma wurin da za a kai sumunti farashin zai iya tashi, amma kamfanin zai cika alkawarinsa inda zai ci gaba da sayarwa a kan 3,500.

Rabiu ya ƙara da cewa za a kaddamar da kamfanin sumunti da ke Sokoto a watan Janairun 2024, wanda hakan zai sa ya faɗaɗa kasuwancinsa a faɗin ƙasar.

Ya ce ya kai wa shugaban ƙasar ziyara ne domin yi masa gaisuwar Kirsimeti da kuma na sabon shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *