Za mu dauki mataki a kan masu tare motocinmu suna wawar kaya – NARTO

Spread the love

Kungiyar masu manyan motocin dakon kaya ta Najeriya, NARTO, ta ce daga yanzu ba za ta sake zuba ido tana bari mutane suna tare motocinsu dauke da kaya suna daka musu wawa ba.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata hira da BBC ta yi da shugabanta Alhaji Yusuf Othman, inda yake kokawa a kan yadda ake samun karuwa a hare-haren da ake kai wa manyan motoci da ke dauke da abinci a wasu jihohin kasar.

Kungiyar ta ce matsalar ta kai matakin da ba za ta zauna tana gani ana sace musu kayan da suke dako ba da sunan wai na gwamnati ne.

Shugaban ya ce, kayan da suke dauka ba na gwamnati ba ne kamar yadda wasu jama’a ke fakewa da haka suna tare motocinsu a sassa daban-daban na kasar suna daka musu wawa wai saboda tsananin rayuwa da ake ciki.

Kungiyar ta ce suna nan suna tattaunawa da duk wadanda ya kamata domin daukar mataki kan yadda za su bullo wa lamarin domin a cewarta ba zai yiwu mutanenta suna aiki ana fada musu suna yin asara ba.

An kama ƴansintiri 10 kan zargin kashe limamin garin Mada

Yan sandan Kano sun cafke Mutane 178 cikin watanni 2 bisa zargin aikata laifuka maban-banta

Alhaji Usman ya ce ba za su daina dakon ba saboda su ma ta nan suke cin abinci, amma za su dauki matakan da suka hada da tafiya a rukuni.

‘’Za mu dauki kwararan matakai duk wanda ya tare mu mu ma mu san muna da shiri. Ba za mu yarda mota ta rika tafiya ita daya ba sai dai su yi layi su yi gungu, idan ma mutane da yawa suka tare su su ma su tsaya su yi kokari su yake su.”

Shugaban ya ce a yanzu ba karamar matsala suke ciki ba sakamakon jama’a suna neman su fi karfinsu a aikin da suke yi na dakon kayan ‘yan kasuwa daga Legas zuwa arewa ko daga arewa zuwa Legas.

Ya ce ba wai a yanzu suka fara gamuwa da wannan matsala ba, ‘’daman can muna samun wannan matsala da barayi a kan hanya to amma wadanda ke kan hanya a yanzu ba barayi ba ne.’’

‘’Mutane sun yi yawa a kan hanya saboda yawan matsalar da ake ciki suka dauki doka a hannunsu duka bin da suka samu su kwace,’’ in ji shi.

‘’Kaya ne na ‘yan kasuwa na dako da muke daukowa daga Legas ko Ibadan ko Ogun zuwa arewa. Ko kuma mu dauki masara ko shinkafa daga Kano ko Jigawa da dai sauransu zuwa Legas,’’ in ji shugaban kungiyar.

Ya ce, ‘’su ne fa ake tarewa ake kwacewa wannan ba ruwan gwamnati kayan jama’a ne ake kwacewa a kan hanya.’’

Shugaban kungiyar ta NARTO ya ce abin har ma ya kaia ana y iwa motocin dakon mai, ba na kaya kadai ba.

Ya ce wannan ne ma yake sa ake ganin wani lokacin motar mai na kamawa da wuta. Saboda ko ya ta samu matsala da rami a hanya ba ta fadi ba sai mutane su zo suna dibar mai da bokiti da sauran abubuwa ana haka sai wuta ta tashi.

Shugaban ya ce akwai lokacin ma da ake kwace musu mota da kaya sukutuk a hanya.

Ya bayar da misalin cewa idan mota ta dauko kaya daga Legas ta fito da sassafe zuwa hanyar Ibadan to za a iya kwace motar da ma kayan duka.

‘’Idan kuma ka bar Ibadan tsakanin Ibadan da Ogbomosho da Oyo shi ma in ka biyo nan in ka yi sakaci za a kwace maka mota,’’ ya ce.

Ya kara da cewa, ‘’idan ka zo Kaduna tsakanin jankshan din Zariya zuwa Kano shi ma in ka bi dare za a kwace maka mota. Tsakanin Abaji da Gwagwalada shi ma in ka yi dare ka yi sakaci za a kwace maka mota da kaya.’’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *