Za mu haɗa kan arewa da samar wa yankin mafitar siyasa – Shekarau

Spread the love

 

Wata sabuwar ƙungiya ta wasu gogaggun ‘yansiyasa a arewacin Najeriya, ta ce ta fara lissafin samar da mafita ga yankin.

Wasu da suka kira kansu masu kishin arewacin Najeriya sun ɓullo da sabon yunƙurin ne da nufin sama wa yankin ingantaccen shugabanci da alkibla ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.

Sun kira wannan yunƙuri nasu da taken ”League of Northern Democrats”, a turance – wani taron dangi na wasu masu fada a ji na areawacin Najeriya, da suka hada da tsofaffin gwamnoni da ma’aikatan gwamnati da ‘yansiyasa da tsofaffin sojoji da ‘yan sanda, da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.

Taron da suka gudanar a Abuja ranar Talata, ya amince da naɗa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau a matsayin jagora.

Mahalarta taron sun ce sun yi la’akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ƙasar wadda ta ƙara nuna wa duniya irin girman ƙalubalen da yankin arewa ke fuskanta.

“Yunwa da talauci da jahilci ne suka addabi yankin arewa,” a cewar ɗaya daga cikin mahalarta taron, Danburan Zazzau, Muhammad Sani Sha’aban, wani ɗansiyasa daga jihar Kaduna.

“Ana ta surutun cewa arewa ta lalace, matasa sun lalace, ba shugabannin kirki, ana ta sace kudaden mutane, shi ya sa muka tsinto masana, gogaggu a fannoni daban-daban mu kusan 200,”

“Babbar manufarsu ita ce, waɗanne matakai za mu ɗauka na faɗakar da al’ummar arewa game da mutanen da ya kamata su shugabance su,” in ji Shekarau.

Hajiya Inna Maryam Chiroma, wata jigon siyasa a jihar Barno ta ce halin da ake ciki a yankin arewacin Najeriya, abin a tsayawa ne a duba, don a kawo gyaran da ya dace.

“Dole ne mu tsaya, mu zana abubuwan da suke damun arewa, sannan shugabannin yankin su zauna su hada kai su fuskanci matsalolin yankin,” in ji ta.

Sun ce ɗaya daga cikin babbar manufarsu ita ce haɗa kan al’ummar arewa da samar wa yankin mafitar siyasa.

A cewar ƙungiyar, hadin kan arewa ne zai zama ginshiƙin farfaɗo da arewa a matsayin jagaba a fagen siyasar Najeriya.

Yankin arewacin Najeriya dai na fuskantar tabarbarewar al’amura da koma-baya a fannoni da dama na ci gaba, musamman tsaro da ilimi da tattalin arziki.

Amma wasu masu sharhi sun bayyana wannan yunƙurin na ƙoƙarin farfaɗo da yankin a matsayin wata manufar siyasa, kuma ƙungiyar na iya rikiɗewa ta koma wata jam’iyyar siyasa idan tafiya ta yi tafiya, musamman la’akari da rarrabuwan kan shugabannin yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *