Za mu iya mayar wa maniyyata rarar kuɗi saboda karyewar dala – NAHCON

Spread the love

Shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuɗin da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka.

Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis.

“Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kuinka ka saka ne ranar da take naira 900, to ai ka ga akwai ranar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata ma mu maida maka. Ba mu jira tana ta yin asa ba. To idan kuma ta ara yin sama fa?” In ji Jalal Arabi.

Ya ara da cewa “indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan hakkin kowa ba da iznin Allah. Za mu tabbatar mun biya wannan rarar.”

To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya ba faɗi lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuɗaɗen nasu ba.

A mafi yawancin lokuta dai hukumar ta Alhazai kan mayar wa alhazai rarar kudaɗen ne bayan kammala aikin Hajji.

A yanzu haka dai naira na ci gaba da samun tagomashi a kan dalar Amurka inda bayanai ke nuna farashin dala a kasuwar bayan fage na tsakanin naira dubu ɗaya da ƙasa da haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *