Za Mu Kawo Karshen Matsalar Tsaron Da Ake Fuskanta A Nigeria: Taoreed Lagbaja

Spread the love

Babba hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar, Taoreed Lagbaja ya tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa nan ba da jimawa ba sojoji za su kawo karshen matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Janar Lagbaja ya bayaya hakan ne cikin jawabin da ya yi a lokacin bikin rufe babban taron rundunar sojin ƙasa ta Najeriya na shekarar 2024 da aka gudanar a jihar Akwa ibom da ke kudancin ƙasar.

Taron na kwanaki biyar – wanda manyan hafsosjin rundunar sojin ƙasa ta Najeriya suka halarta ya duba irin nasarori da rundunar ke samu, da kuma irin tsare-tsare da rundunar ke yi wajen gudanar da ayyukanta a faɗin ƙasar..

DANDALIN KANO FESTIVAL

”Ina son tabbatar muku cewa rundunar sojin ƙasa ta Najeriya na kan hanyar kawo ƙarshen matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta”, in ji Janar Lagbaja.

Ya ƙara da cewa ya samu wannan tabbaci ne sakamakon irin bayanan da yake samu daga sassa daban-daban na rundunar a faɗin ƙasar.

Tun da farko babban hafsan sojin ƙasan ya yi watsi da kiraye-kirayen da ya ce wasu da ya kira ”masu son rai na yi wa sojoji na kawo ƙarshen mulkin dimokraɗiyya”.

Ya ce a yanzu abin da ke gaban rundunar sojin Najeriya shi ne maido ta martaba ta ƙimarta, bayan shafe shekaru masu yawa suna jagorantar ƙasar, don haka ya ce sojojin ƙasar ba za su yi abin da zai zubar musu da ƙimar da suka yi shekara 25 suna ginawa kansu ta hanyar barin wanzuwar mulkin dimokraɗiyya a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *