Za mu kawo ƙarshen talaucin da ya yi wa Najeriya katutu nan da 2030 — MDD

Spread the love

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta taimaka wa Najeriya ta ga bayan talauci da ya yi wa al’ummar ƙasar katutu.

MDD ta ce za ta cimma hakan nan ta hanyar bin tsare-tsaren ci gaban muradun ƙarni wato (SDG) nan da zuwa shekara ta 2030 kamar yadda aka tsara.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wakilin Jin-ƙai na MƊD a Najeriya, Mohamed M. Malick, a lokacin da yake jawabi a Abuja a yayin taron cikar Majalisar Ɗinkin Duniya shekaru 79 da samar da ita.

Malick ya kuma yaba wa gwamnatin Najeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samar da tsare-tsare sama da talatin daga MDD da za su yi tasiri a Najeriya.

Ya ce, “muna fatan cimma burinmu nan da shekara ta 2030 kuma za mu ci gaba da bai wa ƴan Najeriya tallafi a kowane ɓangare domin inganta rayuwarsu kamar samar da ilimi mai inganci, yaƙi da fatara, sauyin yanayi da wasu cututtuka.”

Ministan Matasan Najeriya, Ayodele Olawande wanda ya yi jawabi a madadin Gwamnatin Tarayya, ya ce akwai buƙatar masu ruwa da tsaki su taka mahimmiyar rawa wajen inganta rayuwar matasa don su samu kyakkyawar makoma a gobe.

Ministan ya ce, Nijeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da tarin matasa waɗanda kaso kusan 70 ba su haura shekaru 35 ba kuma suna da zimmar kawo sauyi a ɓangarori daban-daban na rayuwa da za su samar da ci-gaba.

Duk da ƙalubalen da tattalin arziƙin da Nijeriya ke fuskanta, Ministan ya ce gwamnati da haɗin-gwiwar MDD tare da masu ƙoƙarin kawo sauyi mai amfani ga al’umma su na aiki tuƙuru wajen samar da hanyoyin inganta ƙirƙire a tsakanin matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *