Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ce ta yi maraba da hukuncin kotun ƙolin ƙasar wadda ta umarci gwamnonin su daina riƙe wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu da ake ware musu daga asusun gwamnatin tarayya.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman ya ce ƙungiyarsu za ta yi biyayya ga hukuncin kotun, yana mai cewa a yanzu lauyoyinsu sun buƙaci kwafin hukuncin kotun wanda za yi nazari a kai.
Ya ƙara da cewa gwamnonin na murna da karkasa iko dangane da ‘yancin ƙananan hukumomin.
”Hakan zai rage wa gwamnoni nauyi, mutane ba su san yadda jihohi ke kashe maƙudan kuɗi wajen ɗaukar ɗawainiyar ƙananan hukumomi ba ”, in shugaban ƙungiyar gwamnonin ƙasar.
Da dama dai na ganin wannan hukunci zai shafi jihohin ƙasar, musamman yadda suka saba riƙe kuɗin ƙanannan hukumomin da kuma ayyukan da suke yi.
To sai dai gwamnan na Kwara ya kare matakin da cewa hakan ba zai shafi jihohin ba, musamman jiharsa ta Kwara da ya ce dama ƙananan hukumomi na da ‘yanci, saboda dama a cewarsa ba ɓarnatar da kuɗin ƙananan hukumomin gwamnonin ke yi ba.
”Don haka yanzu sai ƙananan hukumomin su ci gaba da riƙe kansu, musamman a wannan lokaci da ake dab da tabbatar da mafi ƙanƙantar albashi, su tabbatar suna biyan albashin ma’aikata sannan sarakunan gargajiya su sami kashi 5 cikin 100 kuɗin da ake bai wa ƙaramar hukumar, waɗannan su ne manyan batutuwan”.
Wani ɓangare na hukuncin shi ne haramta wa jihohin rusa zaɓɓaɓun shugabannin ƙananan hukumomin.
Kan wannan batu shugaban ƙungiyar gwamnonin ya ce wannan zai shafi wasu gwamnonin, musamman waɗanda ba su da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin a yanzu.
A ranar Alhamis ne dai kotun kolin ƙasar ta yanke hukuncin bayan da gwmanatin tarayya ta shigar da gwamnonin ƙara don su bai wa ƙananan hukumomin ‘yanci, bayan da aka zargi gwamnonin da riƙe kuɗaɗen nasu.