Rundunar yan sandan jahar Kano, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron jahar sun bayar da tabbacin bayar cikakken tsaro yayin gudanar sa
zabukan cike gurbi a kanana hukumomi 6, na Mazabu 3, da rumfunan zabe 66 dake jihar.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a shelkwatar rundunar dake Bompai bayan kammala wata ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaron jahar a ranar Laraba.
Muhammad Gumel, ya ce rundunar za ta yi kokarin bada tsaro mai inganci wajen ganin al’ummar yankunan da za’a sake zabukan masu kada kuri’ar sun yi zabensu ba tare da wata barazana ba.
“Mu a matsayinmu na jami’an tsaro, bamu da niyyar mu hada kai domin a zalinci ‘yan kasa wadanda suka zabi abinda suke so, wannan shi ne burin mu kuma da yaddar Allah haka zamu yi”-Inji Cp Gumel.
Acewarsa suna ci gaba da tattaunawa domin hada kai da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC, wajen ganin anyi zabe na gaskiya don kaucewa amfani da kudi wajen siyan kuri’a.
CP Gumel, ya kuma yi gargadin cewa duk wata hukumar tsaron da bata gwamnatin tarayya ba, bata da hurumin bayar da tsaro, a yayin gudunar zabukan kamar yadda yake a tsare-tsaren dokokin zabe, inda ya bukaci hadin kan jama’ar jihar Kano, wajen ganin anyi zaben an kammala cikin nasara.
Kananan hukumomin da za a gudanar da zabukan na cike gurbi a ranar 3 ga watan Maris 2024 sun hada da, Kunci da Tsanyawa, Rimingado da Tofa sai Kura da Garun Malam.
” Muna tabbatar wa da jama’ar Kano cewa muna da karfin tafiyar da wannan zabe ba tare da wani tashin hankali ba, kawai hadin kan jama’a muke so”CP Gumel”.
Ya ce dukkan abubuwan da suke bukata daga hukumar zabe INEC , sun tabbatar mu su guraren da za a kai kayan zaben harda horas da jami’an da za su jagaranci aikin.
Sai dai kwamishinan yan sandan ya ce , da wahala a sanya dokar takaita zirga-zirga a jahar Kano , kasancewar kananan hukumomi 6 ne , kachal za a gidanar da zaben.
Anasa bangaren kwamishinan zaben Kano, Ambasada Abdussamad Audu Zango, ya ce sun shirya dukkan abunda ake da bukata , kuma hukumomin tsaro sunanan don ganin an yi lafiya.