Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Hon. Tajudeen Abbas ya ce majalisar za ta gudanar da cikakken bincike kan ingancin man da masu ababen hawa ke amfani da shi a faɗin ƙasar.
Hon Tajudeen ya bayyana hakan ne a yau Asabar yayin wata ziyara da ya jagoranci shugabannin majalisar wakilan ƙasar zuwa matatar mai ta Dangote da ke birnin Legas, kamar yadda Gidan talbijin na Channel ya ruwaito.
Kakakin majalisar na wannan maganar ne bayan gwajin ingancin man disel da aka yi a gabansu lokacin ziyarar tasu zuwa matatar.
Tun da farko dai shugaban matatar Alhaji Aliko Dangote ne ya yi wasti da wani zargin da ke nuna cewa man da ake tacewa a matatar tasa bai kai ingancin da ake buƙata ba.
Domin tabbatar da iƙirarin nasa, Dangote da tawagar ma’aikatansa sun gudanar da gwajin man dizel da aka sayo daga wasu gidajen mai biyu da kuma wanda matatar ke tacewa a ɗakin gwajin ingancin mai da ke matatar.
Bayanai sun ce an sayo man ne a gaban jagororin majalisar, sannan aka ɗauki na matatar Dangoten ma a gabansu domin kawar da shakku.
Shi dai mai marar inganci, masana na gargaɗin cewa amfani da shi ka iya lalata injinan ababen hawa.
Sakamakon binciken ya nuna cewa man Dangote ya fi inganci fiye da na sauran gidajen mai biyu da ka shigo da shi ƙasar daga waje, kamar yadda Channels din ya ruwaito.
Dangote ya ce sakamakon gwaji alamu ne da ke nuna cewa man da ake shigar da shi ƙasar ba shi da ingancin da ake buƙata.